sainayi instagram

SAI NAYI INSTAGRAM.1

Asabe ta yi tagumi gami da tsaki, sannan ta kara kallon kanta a Mudubi, ta mike tsaye ta juya ta kara juyawa , sannan ta kara zama. "Mai Lariya da Lami suka fini dashi, Na fisu komai kyau fari da Diri, amma saboda kawai suna rike wayar da take Instagram, Tacno , sune kullun gorin yau da ban na gobe daban, kuma ma ita Lamin ai ta nuna min photon da tasa wanda muka yi ni da ita an yi mata LIKES sama da 1000. kuma nasan danni ake yi matan.

Asabe dai ba 'yar kowa bace gidansu dai-dai gwargwado akwai tarbiya, Babanta ya mutu, Babarta ta tsaya sosai akanta dan ta san lallai wannan lokacin 'Da namiji ma sai ka dage bare mace kuma budurwa,
Saboda rashin tsayayyen miji Babarta ta barta take karatun N C E , a FCE to anan ne ta gamu da wadannan kawayen LAMI DA RALIYA .
Bayan ta gama wannan tunani Sai ta yankewa zuciyar ta cewar , in har Lami da mairo zasu rike TACNO,ita kuma ai sai dai SAMSUNG GALAXY S3 ko GALAXY NOTE2, ta yanke wa kanta shawarar ko ta halin kaka sai ta mallaki daya daga cikin biyun wandan nan wayoyin, ta mike tsaye gami da kallon mudubi a karo na 2, ta fada a zuci, bahaushe yace da ruwan ciki ake jan na rigiya,
can sai taji Nokiarta (C1) ta dau kara tana fadin , TALAKANNAN TALAKANNAN TALAKANNANNNnnnn...

Ta daga cikin bacin rai....
........ A daya bangaten Raliya..cikin zumudi da shewa ta fara, " ke shegiya tun dazu nake ta neman layinki yaki shiga ko batir dinne ya goce? Asabe tai shiru bata ba ta amser ba sai kusan minti 1 , Raliya ta kara magana 'yar rainin hankali mai kike ne kikai min shiru? dama gaya miki zanyi mitumin ya canzamin waya GALAXY X3, Shine na rokeshi ya barmin tsohuwar TACNO din na bar miki,shine yace sai dai idan kun hadu ya baki da kansa.
Sai anan Asabe tai magana "Raliya kice masa ya rike abarsa bana ma so bare har yace sai munhadun, tai tsaki. Raliya taji haushi dan ita a tunaninta ma har tukwici zatai mata ta fada a zuci, sannan ta tace banza uwar fadin RAI.. sai anjima ma hadu a makaranta, ta kashe wayar.

Bayan ta ajiye wayar sai ranta ya dada baci , wai ni zaai wa kyautar tsohuwar waya .. hehehe tai dariya kuma , ai nafi karfin tsohuwar waya yasin , wannan ma Nokiar ni naga dama,

wayarta ta kara ringi, tana dubawa sai taga sunan wani tsohon Saurayinta Alh Ilu Naira, abin mamaki dama shi ta fara kawowa a zuciyarta,

saboda tsabar saurin ta daga wayar sai wayar ta fadi kasa har sai da cikon da taiwa batir din ya cire, nan dai cikin sauri tai ta kokarin mayar da batir din kar ya dauka kashewa tayi, kuma shirinta ya watse.....

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA