nageria tazama.....
A yayin da kasashen Amurka, Birtaniya, Chana, Faransa da kuma Isra’ila suka fara jibge dakarun sojinsu a Nijeriya domin lalubo bakin zaren maboyar ‘yan matan sakandiren Chibok da ke jihar Borno da kungiyar Jama’atu Ahlus Sunnah Lid’dawati Ilal-Jihad, wadda aka fi sani da Boko Haram ta yi garkuwa da su. Shi kuma a nasa bangaren shugaban kungiyar, Imam Abubakar Shekau ya fitar da wani faifan bidiyo a ranar Litinin din da ta gabata wanda hakan ya zo daidai da kwanaki 28 da bacewar ‘yan matan.
A cikin faifan bidiyon da ya yi magana da harshen Larabci da kuma Hausa na tsawon kimanin mintuna 27, an nuna kusan ‘yan mata da yawansu ya kai kimanin 130 kowacce sanye da Hijabi a zazzaune suna karanta Suratul Fahiha kana kuma wasu biyu ribe da tuta mai taken kalmar ‘Shahada.’
A cewar Shekau ya Musuluntar da kusan dukkan’yan matan da ba Musulmai ba ne. A rahotannin baya an yi kiyasin sama da mata 270 ne ‘yan kungiyar suka yi garkuwa da su a makarantar sakandiren mata ta Chibok ranar 14 ga Afirilu, wanda aka ce guda 53 daga ciki sun samu nasarar tsira bayan wasu kwanaki. “Abin da kawai zan iya cewa shi ne, idan kuna bukatar na saki ‘yan matan da na kama, dole ku sakar min yara na da ku ka kama Borno, Yobe, Kano, Kaduna, Abuja, Legas har zuwa Enugu.
Akwai ma wasu daga ciki da su ka dauki tsawon shekaru biyar ba tare da sun ga matansu da ‘ya’yan su ba. Akwai ma matar da ku ka saka amma kuma ku ka hana ta tafiya da ‘yar ta. Shin don Allah ba na yi garkuwa da wasu ba domin a sake su. Baya ga haka Allah ne Ya sa ni yin wannan garkuwar. Ku da ku ka kama min mabiya tsawon shekara biyar, ku ka tsare mace shekaru hudu zuwa biyar ba tare da ta yi aure ba. Ku ka kuma kama tare da tsare mana ‘ya’ya,” cewar Shekau.
Duk da dai bai bayyana adadin ‘yan matan da su ke hannun sa ba, Shekau ya ayyana cewa lallai ya Musuluntar da kusan dukkansu yayin da ragowar ma suna kan hanya. “ Sai na sayar da su. Na kuma maimaitawa. Na kuma rantse da Allah ba za ku kara ganin su ba, har sai zuwa lokacin da ku ka sakar min yara na da ku ka kama tare da tsarewa.
Sai da dukkan alamu zai yi wuya a gane ko Shekau na tare da ‘yan matan a waje guda ko kuma a wani waje daban ya ke da su. Domin yanayin hoton faifan bidiyon ya nuna su a wani waje mai kama da daji ne. Yayin da shi kuma hoton sa ya bayyana a yanayin wajen da za a iya ayyana a wani rufaffen waje. Sai dai kuma gwamnatin tarayya ta yi baki biyu a yayin mayar da martani game da wannan faifan bidiyo.
A yayin da Darakta Janar Mista Mike Omeri na hukumar wayar da kai na kasa ya ke cewa; “Gwamnati na yin dukkan mai iyuwa domin nazarin damar da ‘yan kungiyar su ka bayar na ganin an dawo da ‘yan matan gidajen su lami lafiya. Bayanan farko da wasu kafafen yada labarai su ka fitar na cewa daga gwamnati ne, ko kadan ba gaskiya ba ne”. Jim kadan da fitar faifan bidiyon Ministan harkokin cikin gida Abba Moro ya ayyana cewa, gwamnatin tarayya ba za ta taba mika wuya ga ‘yan ta’adda ba.
“Kamar yadda kowa ya sani mun gayyaci kasashen waje, kuma muna nan mun kusa isa inda su ke. Babu kokwanto kowa ya matsu ya ga ‘yan matan nan sun dawo gida. Amma komai akwai sharadin da ake amfani da shi,” in ji Moro.
Wannan kama ‘yan mata ya hada hankalin duniya, ciki kuwa har da sanannun Malami na duniya. Sai a cewar Shekau, duk wadannan Malamai ba Malaman gaskiya ba ne face kawai ‘yan siyasa. Kana kuma manyan kasashen duniya irin su Amurka, Birtaniya, Chana, Faransa da kuma Isra’ila sun yi alkawarin taimakon Nijeriya. Amma duk da haka Shekau ya yi ikirarin babu wata runduna da za ta iya gano inda ya ke ballantana ta tseratar da ‘yan matan. Ya kuma kara da cewa, ya girgiza ganin yadda kasashen duniya su ka fusata dangane da wannan batu.
Wasu daga cikin ‘yan matan da aka tattauna da su a cikin faifan sun yi bayani kamar haka;
Yarinya Ta Farko
Yaya sunan ki?
Hauwa.
Hauwa wa?
Hauwa Abdu.
Ya sunan yaran ki?
Kwantai.
Ke Krista ce?
Eh.
Yanzu kin karbi Musulunci yaya sunan ki?
Halima.
Me ya sa ki ka karbi Musulunci?

Comments
Post a Comment