kungiyar arsenal
Kungiyar Arsenal na zawarcin 'yan kwallon Barcelona Alexis Sanchez da Pedro. Mujallar The Daily Mail tace Arsene Wenger na fatan dauko 'yan wasan biyu idan har Barca zata sayar da 'yan kwallon cikin farashi mai sauki. Sanchez, mai shekaru 25, yana fama da rashin buga wasanni da yasa yake hangen komawa wasa a Premier Ingila da ake ganin zai kai £20million. Shi kuwa Pedro, mai shekaru 26, ya zura kwallaye 16 da hakan yasa Wenger ke son dauko dan wasa domin kawar da matsalar rashin zura kwallo a kungiyar
Comments
Post a Comment