karmin Labari

KARAMIN LABARI MAI CIKE DA GARGADI.

Wani mutum ya kira 'Dansa
yace masa "zo ka
rakani unguwa" sai yaro yace
"toh" suka tafi. Suka kama
hanya suna ta tafiya har yaro
ya gaji yace "Baba, wai ina
zamu ne da nisa haka? Sai
baban yace "ai mun kusa"
Can sai suka isa wajen wata
katuwar
bishiyar mangwaro dake cikin
gonar wani, sai uban yaba
yaron buhu yace tsaya nan zan
hau idan kaga wani ya taho ka
fada min don in sakko da sauri,
kaji? Yaro yace "toh" sai Uban
ya tattare wando ya hau
bishiyar ya miqa hannu zai
tsinki na farko kenan sai dan
yace "Baba ga Wani fa Yana
kallonmu, sai baban yayi maza
ya sakko amma bai ga kowa ba
sai yace da yaron "kace Wani
na kallonmu, ina yake? don
banga kowa ba. Sai yaro yace
"Baba ai a makaranta ne malam
yace mana ALLAH Yana ganin
kowa da kowa harda ma
6arawon da zai saci kayan
wani"
sai baban yayi shiru jin kalamin
yaron nan sannan ya fasa satar
kuma yayi wa ALLAH godiya da
Ya bashi yaro mai kaifin hankali
da basira wanda ya tunatar
dashi tsoron Allah.
Ya ALLAH muna rokonKa Ka
bamu yara masu hankali da
natsuwa wadanda zasu dinga
tunatar damu muji tsoronKa,
AMEEN!!!

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA