jamiai na nema su hana zanga zangar daliban chibok
Jami'an 'Yan Sanda Na Neman Hana Masu Zanga-zangar Sace Daliban Chibok A Abuja.
A ci gaba da zanga zangar luma a da wasu fitattun mata ke gudanarwa, Jami'an ‘Yan Sanda sun hana masu zanga-zanga shiga dandalin Unity Fountain da ke Abuja a yammacin Lahadi yau, inda ma suka yi ta ja-in-ja da mata da maza.
“A matsayina na ‘yar Kasar nan, ina da ‘yancin gudanar da taron lumana, babu wanda ya isa ya hana ni wannan daman. Ba zan je ko ina ba. Ina da ‘yancin zuwa ko ina a cikin al-ummarnan. Wannan demokradiyya ce, kuma ko lokacin mulkin soja nayi zanga-zanga, balle demokradiyya. Bazan je ko ina ba,” a cewar Oby Ezekwesili.
Hadiza Bala, daya daga cikin shuwagabanin masu gangamin cewa ta yi “muna nan a wajen da muke zuwa kullum, domin tattaunawa, da gangamin lumana, kuma an hana mu, an ce wai mu tafi, mu kuma mun ki, saboda ba za mu bar kowa ya keta hakkin mu na bil adama ba. Na gode.”
“Ba za mu je ko ina ba, kuma duk wanda yake son tafiya ya je, amma ni Oby Ezekwesili, ba zan je ko ina ba. Babu inda zani,” a cewar Ms. Ezekwesil

Comments
Post a Comment