chibok

Wasu daga cikin gungun ‘yan mata daliban
makarantar sakandaren da ‘yan ta’adda
suka kaiwa hari a jihar Bornon Nigeria, sun
yi bayanin yadda suka yi sa’ar kubuta daga
kangin daga ‘yan Boko haram suka yi
wajen shirya kamesu a gidajen kwanansu
na makaranta.
Dalibar wadda muka boye sunanta tace "yayin
da aka kaimu wani daji sai su ‘yan matan suka
fara tunanin cewa tun da wasu daga cikin ‘yan
matan da aka kama sun yi tsalle daga cikin
motar domin kubuta kuma Allah Ya basu sa’ar
kubutar, mai zai hana muma mu jarraba yin
tsallen domin mu kubuta koda kuwa ‘yan
ta’addar zasu kashemu a lokacin? Domin yanzu
dai bamu san inda ‘yan bangar zasu kaimu ba,
don haka sai ini da kawata muka tari aradu daka
muma yi tsalle daga cikin motar suka tsere da
gudu."
Kutsawa da ‘yan banga suka yi har suka sace
dalibai ‘yan mata hakan yaketa haddin
mutumcin Bil Adama don haka ya zama wajibi
kan kasa da kasa da suyi wani abu.
Amurka na daga cikin kasashen da yanzu haka
ke bada gudummawar bincike da kayan aiki,
sauran kasashen dake aiki kan haka sun hada da
Birtaniya, kuma hukumomin Nigeria sun yi
alkawarin bada Tukuicin Dolar Amurka dubu dari
uku ga duk wanda ya basu cikakken labarin da
zai taimaka masu sanin wurin da aka kai daliban
aka boye.
Ya zuwa yanzu dai babu bayanai akan makomar
ragowar daliban mata su kusa 300.
Karin Bayani Kan Wannan Batu Najeriya
0 Comments
Fadin Ra'ayi a Wannan dandalin
Cikin Sauti Rumbun Kallo
NAJERIYA
Dalibai mata su hudu na makarantar sakandare na
Chibok,a cikin wanna hoton da aka dauka 21 ga

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA