allah yasa
Za A Kawar Da Kungiyar Boko Haram Cikin Watanni
Uku, Cewar Kungiyar Gwamnonin Arewa Gwamnan jihar Niger kuma shugaban kungiyar
gwamnonin Arewa, Mu'azu Babangida Aliyu ya
bayyana cewa suna tsammanin gwamnatin tarayya
za ta yi maganin kungiyar Boko Haram cikin watanni
uku masu zuwa. Gwamnan ya bayyana hakan ne bayan masu fada a ji
da dama a duniya sun nuna rashin jin dadin su ga
sace dalibaia mata da aka yi da kuma yadda suke ta
Allah wadai da dabi'un kungiyar ta Boko Haram. Gwamna Aliyu ya bayyana hakan ne a yayin zaman
da kungiyar gwamnonin Arewan ta yi da jakadan
Washington DC a Nijeriya da kuma kungiyar sanya
hannayen jari ta Amurka da aka gudanar a otal din
Sheraton a Abuja.
Ya ce "Wannan shine abin da muke tsamman daga gwamnatin tarayya da taimakon kasashen waje, na
yin maganin kungiyar Boko Haram nan da watannin
uku masu zuwa. Kamar yadda ya ce dukkan su sun hada karfi da
karfe domin magance matsalar Boko Haram. Ya ce "
matsalar da kasarmu ke fama da ita a yanzu na
rabuwar kai, bambancin addini, rashin aikin yi,
kabilanci da makamantan na neman hana amsa
sunanmu na uwa ga kasashen Afrika. Bai kamata mu ci gaba da kasancewa a haka ba. Lokaci ya yi da za
mu yi maganin wadannan matsalolin".

Comments
Post a Comment