kamar yah?

A lokacin kyakkyawan Matashin yake zaune shi kadai kamar maye a can qarshen ajin, ya tattara hankali da nutsuwarsa ga fuskar wayarsa, bai lura da wata farar tauraruwar budurwa sanye da zungureren hijabi wacce take tsaye a kansa ba. "Hafizu ina ta magana." Muryarta mai tafiya da hankali, a karo na farko ta baqunci kunnensa. Ya d'ago da kansa ya zuba mata ido. Qwaqwalwarsa ta shiga tariyar wani al'amari da ya faru gare shi a wani lokaci, lokacin da Hadiza tazo masa da baqin albishir wai ya d'irka mata ciki daga kawai taje suyi extra lesson kafin daga bisani ya aikata lahira. Yanayi da halin da yake ciki yanzu ya saje da wancan lokacin, sai dai wannan ba Hadiza ba ce, wannan ta zarce Hadiza komai ta fuskar cikar halitta, wannan farar tauraruwa ce mai haske, mai murmushin sace zuciya. Ta guri d'aya ta kwafsa, ta tashi ta zura wani uban Hijabi kamar matar Liman. Kyakkyawar budurwar ta jefe shi da murmushinta firgita samari. Ya ja gwauron numfashi tare da kawar da kansa daga gareta. "Hafizu wajenka nazo. Jiya ne aka mana wata lakca mai tsauri, shine wata qawata tace mini duk makarantar nan ba wanda zai mini gamsashshen bayani sama da kai." Yayi kasalallen murmushi. Wannan tauraruwar dake gabansa ta zarce duk wata mace da ya taba mu'amula da ita sai dai hijabinta ya tilasta masa yi mata wani kallo daban da wanda yake wa sauran matan da suka taba kusantarsa, wannan yana mata kallon mai kamun kai. "Ya naga kayi shiru? Kada ka damu, kafin nazo an sanar dani cewa kana samun lokacin extra lesson ne kawai in dare yayi." To dawo dashi hayyacinsa. "Haka ne, a ina zamu had'u?" Lokuta da dama shi yake fadawa 'yam matansa inda zasu hadu, amma a wannan karon sai ya tsinci kansa yana fada mata sabanin haka. Tayi walainiya da ido tamkar wacce ke laluben wani abu. "Mu had'u a can bayam kukar shanye du." Hafizu ya zabura tare da zaro ido waje cike da firgici. Kukar shanye du, wata qatuwar kuka ce qunshe da baqaqen aljanu, akwai watarana wani d'alibi yazo ya wuce ta kusa da ita da tsakar dare, sama ko qasa ya nemi kunnensa ya rasa sai da gari ya waye aka tsince su a qarqashin kukar. An ce aljanun kukar ne suka shanyewa wani malamin lissafi hannu da qafa sbd wai in yana gabatar da darasi yana b'ata musu kasafin kud'insu.

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA