Labarin Wata Mata Mai Aikin Gidan Nama

LABARIN WATA MATA MAI AIKIN NAMA Takansance tana aiki a wata masana'antar saida nama ga masu bukata. Wata rana bayan tazo wurin aikinta ta kuma kamala aikin, Sai ta tafi dakin sanyi wato inda ake ajiya naman da ba'a sayarba (meats Cold freezer) don yin bincike akai. Shigar dakin nata ke da wuya sai kofar dakin sanyin ta rufe Ruf. Tayi - tayi ya bude amma ina kofa taQi budewa tayi bugu iya bugun kofar ko Allah zaisa wani yajita ya kawo mata dauki amma ina babu wada yaji. Tayi kuka iya kuka amma ina babu wanda yajita, kuma sanyin dakin yafi karfin dan adam ya iya jure shi zuwa wani lokaci. Gabadaya ma aikatan masana'antar suntafi maana sun tashi a aiki. Bayan kamar awanni 5 Tana daf da mutuwa a cikin dakin sanyi , katsam sai mai gadin masana'antar ya bude kofar. Bayan ta dawo daga hankalinta, sai take tambayar mai gadin Tayaya har kazo ka bude wannan kofar bayan baka ...