Farillan Alwala

. *FARILLAN ALWALA* Farillan alwala guda 7 neh: • Niyya • Wanke Fuska • Wanke hannaye zuwa gwiwar hannu • Shafar kai • Wanke kafafuwa • Cuccudawa • Gaggautawa *SUNNONIN ALWALA* • Wanke hannaye zuwa wuyan hannu • Kurkure baki • Shaka ruwa • Fyacewa • Juyo da shafar kai • Shafar kunnuwa • Sabunta ruwa agaresu • Jeranta tsakanin farillah *MUSTAHABBAN ALWALA* • Yin bismillah • Goga asuwaki • Kari akan wankewa ta farko a fuska da hannaye • Farawa daga goshi • Jeranta sunnoni • Qaranta ruwa a nisa gabobi • Gabatar da dama kafin hau. *AKAN FASALIN ALWALA* • Wanda ya manta da wata farilla daga gabobinsa, idan ya tuno sai ya aikata ta da abunda ke bayanta, idan kuma yayi nisa sai ya aikata ta ita kadai, ya kuma sake abunda ya sallata bayan faruwa...