lipton don amfanin kanka
Afanin lipton ga dan Adam 9. Don Goge-gogen Gida:- Ki zuba ganyen shayinki da ki ka yi amfani da shi a cikin ruwa, idan ya jiku ki goge jikin gado da madubi da kwabobi amma wanda ba a yi musu feshin fenti ba, za ki ga suna sheki da kyalli ko kuma ki yi amfani da jikakken ganyen shayin ki goge . 10. Maganin Rana Da Gajiya:- Idan kin yi aiki a rana kin ga ji, sai ki cika bahonki da ruwa ki jefa ganyen shayin (green tea) da ki ka yi amfani da shi , idan ya jiku sai ki shiga ciki ki yi ‘yan mintuna a ciki har zuwa rabin awa, za ki ji gajiyar duk ta wartsake. 11. Idan kin ci kifi ko kuma kin wanke kifi, kina iya amfani da ganyen shayi domin ya fitar miki da wannan karnin daga hannuki domin wani lokacin ko sabulu ki ka saka hannunki ba zai dai na karni ba 12. Idan an miki allura ko an yi wa yara allura, idan wajen ya kumbura yana zafi, ki na iya saka ganyen shayi a wajen, zai rage zafin , idan ma da kumburi ne ya rage 13. Maganin Warin Baki:- ganyen shayin (peppermint ) da gishiri idan kin h...